Maniyyata aikin hajji zasu fara biyan N1m kudin ajiya

Hukumar jin dadin Alhazai ta Kasa ta nemi duk wani maniyyaci na aikin hajjin 2017 kan ya fara biyan dubu 250 a kowane wata ko kuma ya biya milyan daya kai tsaye ga hukumar jin dadin alhazai na jiharsa.
Maniyyata aikin hajji zasu fara biyan N1m kudin ajiya
Maniyyata aikin hajji zasu fara biyan N1m kudin ajiya
A cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar ta nuna cewa a cikin wannan wata na Disamba ne za a fara biya kudaden kuma a kammala a wata Afrilu na shekarar 2017 a lokacin da hukumar za ta bayyana ainihin kudin kujerar aikin hajjin.
Mai karatu zai iya tuna cewa kudin karamar kujera a shekarar da ta gabata ta zarce Naira miliyan guda ita kanta.
Hukumar ta kara da jan hankalin maniyyatan da su zama masu bin doka da oga da kuma biyayya ga dukkanin dokokin kasa mai tsarki a lokacin aikin hajjin.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Popular posts from this blog

Does Lil Wayne have cancer?

Police dismisses bomb scare in Lagos

Survivor